Melania Trump ta ce mijinta zai tafi da kowa a mulkin Amirka


Matar dan takarar shugabancin na Amirka Donald Trump ta zo da bayanin haka duk da sanin mijinta da nuna banbanci a lokacin kamfe.

Donald Trump da Melania Trump a taron Cleveland na jam’iyyar Republican

Mai dakin dan takarar shugabancin Amirka karkashin jami’iyyar Republican Melania Trump a wani jawabi da ba kasafai ake gani tana irinsa ba a yammacin ranar Litinin ta bayyana mijinta Donald Trump a matsayin wanda zai tafiya da kowa da zarar ya kai ga mulkin Amirka.

Misis Trumph da ke da buri na ganin ta zama matar shugaban Amirka a zaben shugaban kasa da za a yi a watan Nuwamba mai zuwa, ta bayyana haka ne a lokacin babban taron jam’iyyar ta Republican a birnin Cleveland na jihar Ohio:

“Donald a shirye yake ya wakilci dukkanin mutanen Amirka ba kawai wani bangare ba, mutanen kuwa sun hadar da Musulmi da Kirista da ‘yan Amirka masu asali da Afirka da Yahudawa da sauransu.”

Ita dai Melania Trump na daya daga ciki iyalai na Donald Trumph da aka tsara za su gabatar da jawabi a babban taron jam’iyyar ta Republican a Cleveland a wannan mako.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like