MEND na tattaunawa da gwamnati a Najeriya


 

 

A wani mataki na kawo karshen tashe-tashen hankulla da ake fuskanta a yankin Niger Delta, tsaffin mayakan MEND sun ce burinsu shi ne na dawo da kwanciyar hankali.

Kungiyar MEND da ta yi zaman aikata ayyukan ta’addanci kan bututan mai a shekaru na 2000 a Tarayyar Najeriya, ta sanar a wannan Lahadi cewa, ta soma tattaunawa da gwamnatin Najeriya a wani mataki na kawo karshen duk wani tashin hankali da yankin Kudancin kasar ke fuskanta.

Cikin wata sanarwa da ta fitar kungiyar ta ce, ta soma tattaunawar ce ta farko da gwamnati ta hanyar wasu kanfanonin mai da kuma shugabannin tsaro, inda sanarwar ta ce babban burin dai da kungiyar ta sa wa gaba, shi ne na ganin an samu zaman lafiya, mai dorewa da zai ta bada damar bunkasa yankinsu na Neja Delta mai arzikin mai.

Sai dai daga nata bangare kungiyar NDA ta Neja Delta Avenders masu fafutukar daukan fansa, da suka yi ta kai hare-hare kan bututan mai tun daga watan Ferairu da ya gabata, sun ki amincewa su tattauna da gwamnatin ta Najeriya.

 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like