
Asalin hoton, Getty Images
Benjamin Mendy zai kai tsohuwar kungiyarsa Manchester City kara, domin a biya shi miliyoyin kudi, bayan ta daina biyan sa albashi.
Dan kwallon tawagar Faransa, mai shekara 29 ya bar Etihad ne a karshen kakar da kwantiraginsa ya kare, kafin fara wasannin bana.
An wanke shi da soso da sabulu kan zargin fyade da tuhume-tuhumen da suka shafi fyade da aka yi masa.
An ce City ta daina biyan Mendy albashi tun daga Satumban 2021, bayan da aka tuhume shi, sannan aka tsare shi.
Mendy ya koma Lorient, mai buga Ligue 1 a Faransa kafin fara kakar nan, inda kawo yanzu ya shiga karawa uku a sauyin ‘yan wasa na gasar ta Faransa.
Ya koma City daga Monaco a 2017 a kan fam miliyan 52, wanda ya lashe Premier League uku a 2018 da 2019 da kuma 2021.
Wasan karshe da ya buga wa kungiyar Ettihad a Premier League, shi ne na ranar 15 ga watan Agustan 2021.
An tsare Mendy wata biyar, daga baya aka ba da shi beli a Janairun 2022 kafin fara fara sauraren karar a watan Agustan 2022.
A watan Janairu ne aka wanke dan kwallon daga dukkan zargin da aka yi masa.
City ba ta ce komai ba, bayan da BBC ta tuntube ta a kan lamarin.