Mene ne aikin Sarkin Ingila kuma su wane ne iyalin masarautar?Sarki Charles III
Bayanan hoto,

Sarki Charles III

  • Marubuci, Jennifer Clarke
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News

A ranar Asabar 6 ga watan Mayu, Sarki Charles III zai zama sarkin Ingila na 40 wanda za a naɗa a cocin masarautar Birtaniya na Westminister Abbey.

Ya zama sarki ne bayan rasuwar mahaifiyarsa, Elizabeth II, a watan Satumba.

Mene ne aikin Sarkin Ingila?

Sarki a Birtaniya shi ne shugaban ƙasa. Sai dai ikonsa na wakilci ne kuma na je-ka-na-yi-ka, sannan ba shi da ɓangare a siyasance.

Yakan karɓi sakonnin bayanai daga fadar gwamnati a kullum, ciki har da bayanan da ake buƙata kafin duk wata ganawa ko kuma takardu da ke neman sanya hannunsa.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like