Mene ne ke faruwa a APC kan yaƙin neman zaɓen Tinubu?...

Asalin hoton, Getty Images

Tun gabanin zaɓen fitar da gwani da jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ne ake raɗe-raɗin cewa akwai ɓaraka a jam’iyyar game da wanda zai tsaya mata takarar shugaban ƙasa, musamman ma wanda shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ke mara wa baya.

Sai dai duk da nasarar da Bola Ahmed Tinubu ya samu na kasancewa ɗan takara, lamarin bai mutu ba.

Wasu kalamai da ke fitowa daga bakunan makusantan Bola Tinubu, da shi kansa, da kuma ɓangaren makusantan shugaba Muhammadu Buhari na haifar da tababa kan alaƙar muhimman ɓangarorin biyu da ke da matuƙar tasiri kan nasarar jam’iyyar a babban zaɓen Najeriya na 2023.

Hakan ya ƙara bayyana a fili ne bayan kalaman gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufa’i, wanda ya ce “akwai wasu a fadar shugaban ƙasa da ke son ganin ɗan takararmu (APC) ya faɗi zaɓe saboda nasu ɗan takarar bai yi nasara ba.”Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like