
Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist (Multimedia)
- Twitter,
- Aiko rahoto daga Abuja
Azumi, kamar yadda aka saba, shi ne kamewa daga cin abinci da abin sha da kuma tarawa a tsawon rana.
A addinance da kuma likitanci, azumi da ibadun da musulmi ke ƙara azama wajen yin su, suna da matuƙar fa’ida wajen inganta lafiyar jiki.
Baya ga fa’idar azumi a addinance, masana lafiya na cewa azumi yana taimaka wa ɗan’adam.
Dr Muhammad Baba Geidam, wani likita da ke asibitin Mallam Aminu Kano a Najeriya ya ce azumi ta fannin lafiya yana da fa’ida musamman abin da ya shafi rage ƙiba.
Ya ce azumin na taimakawa wajen rage yawan kitse da ke narkewa a cikin jini, “wannan kitse shi yake jawo cutuka kamar toshewar jijiyoyin jini na zuciya da kuma bugawar zuciya.”
Ya ƙara da cewa yawan azumin na iya sanyawa a samu lafawar hawan jini, ga masu ciwon suga kuma, yana taimaka wa maras lafiya wajen daidaita yawan sukarin da ke cikin jini.
Yana kuma ƙara ƙarfin garkuwar jiki.
Sai dai ya ce yin azumin ba tare da kyakkyawan shiri ba, na iya jefa lafiyar mutum cikin hatsari.
Ya ba da misali da yadda rashin yin shirin ke iya janyo raguwar ruwan jikin mutum.
‘Motsa jiki a lokacin azumi’
Game da masu motsa jiki, Dr Muhammad Baba Geidam ya ce matuƙar mutum yana da kuzarin yi, to zai iya yin haka, ba tare da ya jefa kansa cikin garari ba.
Ya ce ga masu cikakkiyar lafiyar da suka saba motsa jiki, suna iya ci gaba da motsa jikinsu, ba tare da sun canza lokacin da suka saba yi ba, saboda kawai suna azumi.
Idan da safe mutum ya saba motsa jiki, zai iya ci gaba da motsa jikinsa da safe.
Ya ba da misali da masu buga ƙwallon ƙafa, waɗanda ya ce suna buga wasa ko da lokacin azumi ne, ba tare da ya rage musu kuzari ba.
Sai dai, likitan ya ce ga waɗanda suke fama da wasu cutuka kamar ciwon suga, ya kamata su kiyayi motsa jiki da rana, lokacin da ake azumi saboda kada sugan jikinsa ya yi ƙasa da sosai, abin da ke iya haddasa musu wata matsala.
“Ko kuma ce bai kamata mutum ya je ya motsa jiki fiye da kima, har ruwan jikinsa ya ragu sosai ba, don kuwa hakan zai iya kawo masa ruɗani a jiki” in ji likitan.
A cewarsa, matuƙar mutum yana son motsa jiki a yanayi na azumi, abu mafi dacewa shi ne ya bari sai bayan ya buɗa baki, ta yadda yana kammala motsa jiki, zai iya neman ruwa ya sha, ko cin wani abu da zai ƙara masa kuzari.
‘Sallolin dare na inganta lafiyar jikin ɗan’adam’
Asalin hoton, Getty Images
Dr Tukur Adam Al-Mannar, Babban Limamin Masallacin Juma’a na Al Mannar da ke Kaduna ya ce akwai tarin fa’idoji daga azumi da kuma wasu nau’o’in ibadu da akan kwaɗaita wa musulmi musamman ga jikin ɗan’adam.
A lokacin azumi, yana da matuƙar amfani musulmi ya ruɓanya ibada kamar tsayuwar dare, baya ga salloli na farilla.
Dr Tukur ya ce sallolin da musulmi ke yi suna da amfani ga lafiyarmu – kamar motsa jiki mutum yake yi a kullum.
“Ga lafiya ta jiki, ga kuma lafiyar ruhi da ƙaruwar imani da samun lada daga wajen Ubangiji” kamar yadda ya faɗa.
Ya bayyana cewa “jikin mutum a lokacin da yake sallah, yana tsayuwa ne a kan ƙafafunsa, yayin da kuma yake ruku’i, duka gaɓoɓinsa na baya da na hannunsa suna lanƙwashewa.
Idan ya je sujjada da ɗagowa daga sujjada da kuma dogara da hannu wajen sauka ƙasa da dogara a kansu wajen ɗagawa, wannan yana nuna kamar motsa jiki ne”.
Ya ƙara da cewa duk wata gaɓa guda 360 na jikin ɗan’adam lokacin da yake sallah da duk wata jijiya suna motsawa.
Malamai suna cewa “raka’o’i 12 da mutum zai yi a sallah, daidai suke da tafiyar minti 30 da likitoci kan ba da shawarar mutum ya riƙa yi a kullum, a matsayin ingantaccen motsa jiki.”
Malamai kuma sun tabbatar da cewa wanda yake yawaita sallah, gaɓoɓinsa za su kasance ba sa yawan sarewa.
Ya ba da misali da salloli masu tsawo kamar na qiyamul layli (sallolin dare) da ake yin kusan sa’a ɗaya ko biyu ana yi.