
Asalin hoton, Getty Images
Fifa, ta bayyana Karim Benzema da Lionel Messi da Kyalin Mbappe cikin ‘yan takarar gwarzon dan kwallon kafa na duniya na 2022.
Za a tuna Benzema kan kwallo 15 da ya ci a Champions League da ta kai Real Madrid ta lashe kofin na 13 jumulla.
Haka kuma tsohon dan kwallon tawagar Faransa shi ne kan gaba a yawan zura kwallaye a raga a La Liga a ba.
Shi kuwa Mbappe, wanda PSG ta lashe Ligue 1 a bara ya ci kwallo 26 a wasa 46 da ya yi wa kungiyar Faransa.
Ya kuma taka rawar gani a gasar kofin duniya a Qatar da lashe takalmin zinare da cin uku a wasan karshe da Argentina ta lashe kofin a bugun fenariti.
Messi kyaftin din Argentina ya taka rawar gani a Paris St Germain tun bayan da ya koma Faransa da taka leda daga Barcelona a 2021.
Ya bayar da gudunmuawar da PSG ta lashe Ligue 1 a kakar farko da ya buga mata tamaula.
Shi ne ya ja ragamar Argentina ta lashe kofin, shi aka bai wa fitatcen dan wasa a babbar gasar tamaula ta duniya ta 2022.
Za a karrama fitatcen dan wasan tamaula na duniya a bana, kan rawar da ya taka tsakanin 8 ga watan Agustan 2021 zuwa 18 ga watan Disambar 2022.
Za a sanar da gwarzon dan kwallon kafa na duniya na Fifa a bikin da za a gudanar ranar 27 ga watan Fabrairun 2023.
An tace ukun daga 14 da aka bayyana a baya, inda aka sa wasu kwararru suka tankade su zuwa ukun karshe da za a fidda gwani.
Za kuma a gudanar da zaben tsakanin koci-koci na tawagar mambobin Fifa da kyaftin-kyaftin da wasu ‘yan jarida da kuma kada kuri’a a yanar gizo ta Fifa.