
Asalin hoton, BBC Sport
Ɗan wasan gaba na Argentina Lionel Messi ya amince da ƙara kwanturaginsa tsawon shekara daya a Paris St-Germain abin da zai bai wa dan ƙwallon mai shekara 35 damar ci gaba da zama a ƙungiyar zakarun Faransan har ƙarshen kakar 2024.
Haka kuma kulob ɗin na PSG ba zai bar ɗan wasan gaba na Faransa Kylian Mbappe, mai shekara 24, ya fita daga ƙungiyar ba a watan Janairu mai kamawa, amma za ta iya sayar da shi a ƙarshen kaka a kan farashin da ya dace.
Kocin Atletico Madrid Diego Simeone ya zuga yunƙurin tattaunawa da ɗan wasan gaban Portugal Joao Felix, mai shekara 23, don sayar da shi bayan ya ce “babu wanda ya zama dole” sai kulob ɗin ya yi da shi.
Arsenal na son ta dauki ɗan bayan Argentina Lisandro Martinez a ƙarshen kaka, sai dai matashin ɗan shekara 24 ya fi son komawa Manchester United don ya sake haɗewa da tsohon kocin Ajax Erik ten Hag.
Chelsea na gab da cimma yarjejeniya da don ɗaukar ɗan wasan tsakiyar Brazil daga kulob ɗin Vasco da Gama Andrey Santos, mai shekara 18.
Manchester United na nuna sha’awa don ɗaukar golan Aston Villa mai shekara 30 Emiliano Martinez, wanda ya ba da gagarumar gudunmawa ga Argentina ta cinye Gasar Kofin Duniya.
Tayin Al-Nassr kan kwanturagin fam miliyan 160 don ɗauko ɗan wasan gaban Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 37, na samun goyon bayan gwamnatin Saudiyya.
Kulob ɗin Jamus Eintracht Frankfurt ya yi iƙirarin cewa Manchester United ta yi musu tayin sayen Ronaldo kafin ya bar Old Trafford.
Manajan Barcelona Xavi ya shawo kan kaftin ɗin ƙungiyarsa kuma ɗan wasan tsakiyar Sifaniya Sergio Busquets, mai shekara 34, don ya ci gaba da zama a kulob ɗin har zuwa ƙarshen kaka, maimakon kammala yunƙurin tafiya wani kulob a gasar Major League Soccer ta Amurka a watan Janairu.
Ana raɗe-raɗin cewa tsohon ɗan wasan gaba na Leeds United Raphinha, wanda ya buga wa ƙasarsa Brazil wasa biyar a Gasar cin Kofin Duniya ta Qatar, akwai yiwuwar zai koma ƙungiyarsa ta Firimiya Lig bayan ɗan ƙwallon mai shekara 26 ya kasa taɓuka abin kirki a kakarsa ta farko a Barcelona.
Manajan Arsenal Mikel Arteta ya ce “lokacin sayen ‘yan wasa wata dama ce” gare shi, daidai lokacin da yake neman hanyoyin rufe ɓarakar da ya samu sanadin raunin da ɗan wasan gaban Brazil Gabriel Jesus, mai shekara 25, ya ji a gwiwa.