Messi zai bar PSG, Man United ta yi tanadi idan ta rasa KaneMessi

Kyaftin din Argentina, Lionel Messi zai bar Paris St Germain, bayan da kungiyar Faransa ta yanke shawarar ba za ta tsawaita zamansa ba. (Foot Mercato – in French)

Manchester United ta tanadi ‘yan wasa uku da za ta taya koda ba ta samu daukar dan kwallon Tottenham, Harry Kane, sun hada da mai tka leda a Eintracht Frankfurt, Randal Kolo Muani da na Roma, Tammy Abraham da dan kwallon Inter Milan, Lautaro Martinez, 25. (FourFourTwo)

Tattaunawar da Tottenham ke yi kan daukar tsohon kociyan Bayern Munich, Julian Nagelsmann ta ci karo da cikas, bayan da kungiyar ba ta da tabbas kan daukar daraktan kungiyar. (Telegraph – subscription required)

Sam Allardyce na tattaunawa da Leeds United kan zama kociyan kungiyar an kuma yi masa tayin ladan fam miliyan daya idan kungiyar za ta ci gaba da zama a Premier a badi a karkashinsa. (Star)Source link


Like it? Share with your friends!

1

You may also like