Olisah Metuh, tsohon kakakin jam’iyar PDP ya isa harabar babbar kotun tarayya dake Abuja a cikin motar ɗaukar marasa lafiya.
Metuh na fuskantar sharia ne kan zarginsa da ake na karɓar kuɗi har naira miliyan ₦400 daga hannun tsohon mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, Kanal Sambo Dasuki, wanda shima ya ke fuskantar tuhuma kan badakalar kuɗin sayo makamai.
Bai halarci zaman kotun ba lokacin da aka saurari ƙarar a makon da ya gabata.
Onyeachi Ikpeazu (SAN) lauyansa ya ce mutumin da yake karewa bai halarci zaman kotun bane saboda an kwantar da shi a asibitin koyarwa na jami’ar Nnamdi Azikiwe dake Nnewi kuma ba zai samu damar zuwa kotun ba.
Ikpeazu ya gabatar da wata takarda da wani likita a asibitin ya rubuto wa kotun amma duka alkalin da kuma mai gabatar da ƙara sun nuna shakku kan sahihan cin takardar.
Okong Ababe, alkalin kotun ya umarci Metuh ya bayyana a gaban kotun ko kuma ya fuskanci barazanar kamu daga jami’an tsaro.