Mexico: Babu Wata Tattaunawa Da Kasar Amurka Akan Batun Gina Katanga Tsakanin iyakokin kasashen Biyu.


4bkb25cb893ce4hvyv_800C450

 

 

Ministan Harkokin Wajen Kasar Mexico Luis Videgaray Caso ya ce; Kasarsa ba za ta yi wata tattunawa da gwamnatin Amurka ba akan gina katanta a tsakanin iyakokinsu.

Ministan Harkokin Wajen Kasar Mexico Luis Videgaray Caso ya ce; Kasarsa ba za ta yi wata tattunawa da gwamnatin Amurka ba akan gina katanta a tsakanin iyakokinsu.

Kamfanin dillancin labarun (AFP) da ya ambato ministan na kasar Mexico a jiya alhamis ya ci gaba da cewa; Kasarsa a shirye ta ke ta bude tattaunawa da Amurka domin ci gaba da kyakkyawar alaka a tsakaninsu, amma ba a shirye ta ke ba ta biya kudin gina katanga  a tsakanin iyakokinsu ko tattaunawa akan haka, kamar yadda shugaban Amurka ya bukata.

Ministan harkokin wajen kasar Mexico yana birnin Washington tare da tawagrsa, a matsayin share fagen ziyarar da shugaban kasar  Enrique Peña Nieto zai kai domin ganawa da  takwaransa na Amukra Donald Trump ,sai dai ya soke ziyarar bayan maganganu da shugaban na Amurka ya yi akan cewa Mexico ce za ta biya kudin gina katanga a tsakanin kasashen biyu.

You may also like