
Asalin hoton, TWITTER/M_EBRARD
Ƙasar Mexico ta tura karnukan da suka ƙware wajen aikin ceto zuwa ƙasar Turkiyyya domin su taimaka wajen ceto rayukan mutanen da suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan gini, bayan da mummunar girgizar ƙasa ta afka wa ƙasar ranar Litinin.
Ranar Talata da safe ne jirgin sama ɗauke da karnuka 16 ya tashi daga ƙasar zuwa Turkiyya.
Ƙasar Mexico, wadda a baya ta sha fuskantar bala’in girgizar ƙasa, na da ƙwararrun karnuka waɗanda ake tura su ƙasashen da aka yi girgizar ƙasa domin taimakawa wajen kuɓutar da waɗanda suka maƙale.
Karnukan sun shiga zukatan al’ummar ƙasar a lokacin da aka samu mummunar girgizar ƙasar a Mexico cikin shekarar 2017, a lokacin da suka kuɓutar da rayukan mutane da dama.
Ɗaya daga cikin fitattun karnukan da suka shahara a ƙasar wajen aikin ceton mai suna Frida ta yi fice a duniya bayan da aka ganta sanye da rigar kariya da takalma tana neman waɗanda suka maƙale ƙarƙashin ɓaraguzan gini a birnin Mexico.
Asalin hoton, Getty Images
Frida ta kasance ɗaya daga cikin shahararrun karnukan ceto a Mexico
Frida wadda ke aiki da rundunar sojin ruwan ƙasar ta ceto rayukan mutum 12 tare da nuna inda gawarwaki 40 suke domin zaƙulo su.
Ta yi wannan bajinta ne a lokacin aikin ceto a girgizar ƙasar da ta faru a ƙasashen Mexico da Haiti da Guatemala da kuma Ecuador.
A yayin da Frida ta mutu sakamakon tsufa a shekarar da ta gabata, aƙalla akwai ɗaya daga cikin takwarorinta da suka yi aiki tare a shekarar 2017 da ke cikin tawagar karnukan da za su je Turkiyya tare da rundunar sojin ruwan ƙasar.
An ga Ecko, ɗan asalin ƙasar Belgium, a filin jirgin saman birnin Mexico tare da sojojin ruwan ƙasar.
Asalin hoton, TWITTER/M_EBRARD
Ecko na ɗaya daga cikin waɗanda aka aike Turkiyya
To sai dai ba sojoji kaɗai ba ne za su je aikin ceton. Akwai tawagar ma’aikatan ceto fararen hula da su je domin taimaka wa waɗanda girgizar ƙasar ta rutsa da su.
Ministan harkokin wajen Mexico Marcelo Ebrard ya ce tawagar ta ƙunshi ƙwararrun masu aikin ceto.
Mista Ebrard ya ce an kammala komai na shirye-shiyen tafiyar tare da taimakon ofishin jakadancin Turkiyya a Mexico.
Asalin hoton, TWITTER/M_EBRARD
Karnukan yayin da suke shirin shiga jirgi domin tafiya Turkiyya
Ba Mexico ce kaɗai ƙasar da ta tura ƙwararrun karnuka domin aikin ceto a Turkiyya da Siriya ba.
Suma ƙasashen Croatia da Jamhuriyar Czech da Jamus da Girka da Libiya da Poland da Switzerland da Birtaniya da Amurka sun alƙawarta kai nasu karnukan.
Domin taimakawa wajen ceto mutanen da ke maƙale cikin ɓaraguzan gine-ginen a Turkiyya da Siriya.
Ana amfani da karnukan ne a wuraren da ake ganin zuwan manyan motocin aikin ceton ka iya kai ga ƙaruwar faɗuwar gine-ginen, lamarin da ka iya jefa rayukan mutanen da suka maƙale cikin hatsari.
An bai wa karnukan horo ta yadda za su shinshino numfashin mutane tare da ankarar da jami’an ceton ta hanyar yin haushi tare da ƙoƙarin tonon ƙasa a dai dai wajen da suka ji numfashin.
Jami’an Mexico sun ce ƙoƙarinsu shi ne ”kare rayuka” yayin da karnukan za su iya shinshino warin gawarwaki da waɗanda suka maƙale cikin ɓaraguzan gini.
Yayin da ake ci gaba da aikin ceton, aikewa da karnukan zai taimaka matuƙa wajen inganta aikin ceton ta hanyar kuɓutar da mutane maimakon gano gawarwakin.