Mike Pence ya ba da shaida kan binciken laifi da ake yi wa TrumpMike Pence

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shaidar da Mike Pence ya bayar wani gagarumin ci gaba ne a cikin binciken aikata laifin da aka shafe shekaru biyu ana gudanarwa kan Trump

Tsohon mataimakin shugaban Amurka Mike Pence ya bayar da shaida a yayin gudanar da binciken aikata laifin da ake zargin yunƙurin da Donald Trump ya yi na sauya sakamon zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2020 da ya sha kaye.

Mista Pence, mai shekaru 63, ya zauna na tsawon sa’oi bakwai a gaban wata tawagar alƙalai a birnin Washington DC, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida wa abokiyar hulɗar BBC, kafar yada labaran CBS ta Amurka ta ambata.

A farkon wannan shekarar ne aka aike masa da takardar sammaci zuwa kotun don ya bayar da shaidar.

An gudanar da tambayoyin da aka yi masa ne cikin sirri.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like