Kamfanin mai na kasa NNPC a ranar Lahadi ya bayyana cewa yana kashe kudin da basu gaza miliyan ₦774 wajen biyan kudin tallafin mai a kowacce rana.Idan aka yi duba da kaiyadajjen farashin da ake sayar da mai a gidajen mai da kuma farashin da ake sayo mai daga kasashen waje.
Wannan bayani na zuwa ne kwanaki kadan bayan da kamfanin ya ki amsa rokon da babban lauya Femi Falana ya yi kan kamfanin ya bayyana kudin da yake kashewa kullum wajen biyan tallafin man fetur.
Kamfanin ya yi nuni da cewa wasu mutane ne kalilan su ke amfana da wannan tallafin da kuma makotan kasashe saboda yadda ake fasa kaurin man zuwa kasashen.
NNPC ya bayyana cewa a kalla a rana amfani da litar mai miliyan 50 a kasarnan.
A ziyarar da ya kai wa Hameed Ali shugaban hukumar Kwastam, shugaban kamfanin, Mai Kanti Baru ya nemi babban kwantirola ya shawo ya ba zuwar gidajen mai akan iyayokin Najeriya domin maganin masu fasa kwaurin.