Minista a gwamnatin Buhari ta ce APC za ta mulki Najeriya har abada


Aisha Alhassan, ministan harkokin mata tace jam’iyyar APC mai mulki za ta cigaba da mulkin Najeriya har abada.

Ministar ta bayyana haka a ranar Litinin bayan rantsar da shugabannin jam’iyyar APC na jihohi 35 ciki har da na jihar Taraba, a sakatariyar uwar jam’iyar dake Abuja.

Alhassan wacce akafi sani da Maman Taraba ta bayyana fatanta cewa jam’iyar APC za ta kwace jihohin Gombe da Taraba a zaben shekarar 2019.

“Zan tabbatar da cewa a shiya ta na yi kokari da izinin Allah zamu karbi jihohin Gombe da Taraba a zaben shekarar 2019 kada ayi magana akan Najeriya saboda tuni jam’iyar APC ce ke mulki kuma APC ce zata cigaba da kasancewa akan mulki har abada,” ta ce.

“Rikici ba bakon abu bane a cikin babbar jam’iya kamar APC da zarar mun kammala babban taron zaben shugabannin jam’iyar na kasa za mu fuskanci jam’iyar adawa ta PDP. Ina kara tabbatar muku APC za ta samu nasara a wasu karin jihohi kamar jihar Taraba.”

Har ila yau ministar ta musalta cewa akwai rabuwar kai a jam’iyar APC ta jihar Taraba.

You may also like