Majiyar tsaron kasar ta Tunsiya tana cewa; Hadi Majzoon ya tsallake rijiya ta baya a wani harin ta’addanci.
Majiyar tsaron kasar ta Tunsiya tana cewa; Hadi Majzoon ya tsallake rijiya ta baya a wani harin ta’addanci.
Jaridar “al-Shoroq’ ta kasar Tunisiyan ta buga cewa; Rundunar musamman wacce ta ke fada da ayyukan ta’addanci ta dakile wani shirin ta’addanci na hallaka ministan harkokin cikin gidan kasar Hadi Majazoob.
Rundunar ta sanar da cewa; “Yan ta’addar sun so kai wa ministan harkokin cikin gidan hari a yayin da ya ke kan hanyarsa ta zuwa gidan mahaifinsa.
Tuni an mika mutanan ne dai ga alkali domin ya gudanar da bincike.