Ministan Sadarwa Ya Fara Yakin Neman Zama Gwamnan Jihar Oyo A Zaben 2019


Adebayo Shitu,ministan sadarwa ya bayyana yakininsa cewa shine zai gaji, Abiola Ajimobi, a matsayin gwamnan jihar Oyo a kakar zabe ta shekarar 2019.

Shitu yayi wannan furuci ne a Ibadan lokacin da yake ganawada yan jaridu jim kadan bayan da ya gudanar da  wani taro da yayan jami’iyar APC da suka fito daga kananan hukumomin Egbeda da Ajorosun.

Ministan wanda ya taba yin takarar gwamna a baya,yace zai karba daga inda gwamnan ya tsaya domin dorawa akan kyawawan aiyukan da gwamnan yake yi. 

A cewarsa shine dan takarar da yafi kowanne kwarewa cikin yan takarkarun da ke neman zama gwamnan jihar saboda irin mukaman da ya rike da kuma siyasa da ya koya daga wurin marigayi Obafemi Awolowo. 

“Na kasance wakili a majalisar dokoki ta jiha a shekarar 1979 na kuma rike mukamin kwamishina na tsawon zangon mulki biyu a jihar nan. Na kuma tsaya takarar gwamna har sau biyu kafin na zama minista.

“Wadannan kwarewa ce da mutum bazai iya siya a kasuwa ba  jihar Oyo tana da cigaba da gogewar da bai ci ace danyen hannu ya jagorance ta ba,” yace. 

 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like