Ministan Yada Labaran Nijeriya Ya Yi Barazanar Gurfanar da Kamfanin Gidan Jarida a Kotu


lai-mohammed

Ministan yada labarai na Nijeriya Lai Muhammad ya yi ikirarin cewa zai dankara kamfanin jaridar Daily Independent a kotu a sakamakon wani rahoto da ta wallafa da ya ce na nufin bata sunan shi.

A rahotan, Daily Independent ta zargi ministan da satar fasahar shirin ‘Change Begin With Me’ da kuma kashe kudade makudai da adadinsu ya kai naira Billiyan 3.4 a kaddamar da shirin.

Haka kuma ministan ya yi barazanar gurfanar da Tsohon shugaban Airtel, Akin Fadeyi da kuma Omo Ba zuaye wadanda suka zarge shi da satar fasahar shirin daga wajensu.

A ranar 8 ga watan satumba ne gwamnatin Muhammadu Buhari ta kaddamar da shirin ‘Change Begins With Me’ a Abuja domin a sauya halayen da ke hana kasar ci gaba. Sai dai shirin ya ci karo da maganganu marasa dadi.

Ministan ta hannun lauyoyinsa Falana & Falana’s Chambers ya bayyana cewa wannan zargi ba karamin bata masa suna ya yi ba.

A takardun da ya turawa kamfanin jaridan da kuma mutane biyun, ya basu kwanaki 7 su janye maganarsu ko kuma su fuskanci kuliya.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like