Ministar Kudi, Kemi Adeosun ta musanta rahotannin cewa ta rubutawa Shugaba Buhari wasika inda ta nemi ya dakatar da biyan dala milyan 16.9 ga lauyoyin Ministan shari’a wadanda suka taka rawa wajen maidowa Nijeriya sama da dala milyan 322 na kudaden da Tsohon Shugaban Kasa, Marigayi Sani Abacha ya boye a Bankin kasar Swiss.
Ministar ta jaddada cewa a ranar 18 ga watan Disamba na shekarar 2017, gwamnatin kasar Swiss ta sanya wadannan kudade a cikin wani asusu na musamman da ke Babban Bankin Nijeriya. Ana dai zargin Ministan Shari’a, Abubakar Malami da makarkashiyar yin amfani da lauyoyin wajen samun wani kaso daga kudaden na Abacha.