Modu Sharif ya gana da Buhari a fadar Aso Rock


Ali Modu Sherif, tsohon shugaban jam’iyyar PDP ya gana da shugaban kasa Muhammad Buhar ranar Alhamis a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Amma kuma ya fice daga fadar ba tare da sanin mutane bayan ganawar da ta dauki tsawon sa’a guda.

Akan hanyarsa ta shiga ofishin shugaban kasar Sherif ya nuna sha’awarsa ta ganawa da manema labarai amma kuma sai ya canza ra’ayinsa bayan da ya fito daga ofishin.

Sherif wanda ya fice daga fadar da karfe 2:40 na rana ta kofar da aka warewa manyan hafsosin sojan kasarnan.

Tsohon shugaban jam’iyyar ta PDP wanda ya sauya sheka ya zuwa APC makonni uku da suka wuce tun da fari ya umarci magoya bayansa da su shiga jam’iyar ta APC.

You may also like