Shakiru Balogun dan takarar shugabancin karamar hukumar Ikotun/Igando karkashin jam’iyar APC ya rasa ransa.
Mamacin yarasa ransa ne bayan da wata mota take shi, ya kuma mutu nan take.
Balogun wanda tsohon shugaban kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi ne reshen karamar hukumar,ya rasa tiketin takara a jam’iyar.
Ance yana kan hanyarsa ne ta zuwa sakatariyar jam’iyar APC a wani bangare na shirye -shiryen zabe lokacin da ya gamu da ajalinsa.
Tuni aka binne mamacin kamar yadda addinin musulunci ya tanada.