Motoci marasa matuƙa sun fara yawo a kan titunan Singapore, inda mutum kan tsayar da su ya shiga kyauta domin yawo.
Hakan dai wani ɓangare ne na gwajin motoci, ko da yake akwai mutum a zaune a kujerar direba.Sai dai motocin da kansu suke tuƙi, matuƙin na lura ne kawai da yadda motar ke tafiyar da kanta, don gudun ɓacin rana.
Wani kamfani, nuTonomy da ke da ofisoshi a Amurka da ƙasar ta Singapore ne ke yin wannan gwajin.Kamfanin ya ƙware ne wajen yin manhajar butun-butumi da fasahar ababen hawa marasa matuƙi.
A farkon wannan shekarar ne kamfanin ya yi wani gwaji a wani ƙaramin gari.Sai yanzu kuma yake wani gwajin tare da ɗaukar fasinjoji.
Gwajin na Singapore na zuwa ne bayan kamfanin motar haya na intanet, Uber ya sanar da fara amfani da motoci masu tuƙa kansu a Amurka.
Sai dai kamfanin Google ya kwashe shekaru tana gwajin mota mai tuƙa kanta a California, amma sai nan da wasu shekaru zata fito da shi ga jama’a.