Mai horar da kungiyar kwallon kafan ta Manchester United, Jose Mourinho ya kawo ziyarar ne a karkashin ayyukan shirin samar da abinci na majalisar dinkun Duniya don ganin yadda karancin sinadarin gina jiki a cikin kayan abinci ke shafar cigaban yara a nahiyar Afirka.
“Nayi mamaki matuka, kuma na kadu da yawan yaran” inji Mourinho yayin da yake tsokaci a Landan dangane da yawan yaranda basu samu abinci mai dauke da sinadarai masu gina jiki.
A zagaye zagayen da ya yi, Mourinho ya kaiziyara kasashe 2, Laberiya da Kwatdebuwa don fahimtar illolin rashin cinabinci mai gina jiki.