Mu Tallafawa Marayun Da Sanata Ali Wakili Ya Bari – Saƙon Sanata Ndume Ga Majalisa


Tsohon Shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa Sanata Ali Ndume ya yi kira da jan hankalin majalisar dattawan Nijeriya da ta tallafawa marayun da marigayi Sanata Malam Ali Wakili ya bari a baya.

Sanata Ndume ya yi kiran ne a wani zama da majalisar ta yi don karrama marigayi Sanata Ali Wakili wanda kafin rasuwar sa yana wakiltar Kudancin Bauchi ne majalisar.

Ya ce “mutuwa na kan kowa kuma ba wanda ya fi karfin hakan ya faru da shi, abin da kawai za mu yi shine mu saka dan wwanmu Sanata Ali Wakili a addu’ar mu kuma mu waiwayi abin da ya bari don tallafawa musu da daukar nauyinsu.

Sanata Ndume ya kuma yi addu’ar Allah ya jikan Sanata Malam Ali Wakili da rahama

You may also like