A ƙalla mutane goma ne suka rasa ransu, 50 kuma suka jikkata sakamakon fashewar wasu abu guda biyu da ake kyautata zaton bom ne a tashar jirgin ƙasa ta ƙarƙashin ƙasa dake St. Petersburg birni na biyu mafi girma a ƙasar Russia.
Kafar yaɗa labarai ta CNN ta rawaito cewa ɗaya daga cikin fashewa ta faru ne a cikin tarago ɗaya na jirgin a tashar Sennaya Ploshad dake birnin.
Mai magana da yawun shugaban ƙasar ta Russia Dmitry Peskov yace tun farko shugaba Putin ya ziyarci birni a yau litinin, amma yanzu yana birnin Strelna dake kusa da birnin na St. Petersburg .
Tuni shugaba Putin ya miƙa ta’aziyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu,ya kuma ci alwashin gano musabbabin harin.
Tuni dai aka rufe dukkan hanyoyim jirgin ƙasa na ƙarƙashin ƙasa dake birnin.
Kawo yanzu dai babu wata ƙungiya da ta ɗauki nauyin kai harin.