Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe mai shekaru 93 wanda kuma ya dauki tsawon shekaru 37 yana shugabancin kasarsa ya bayyana cewa, ya fara yakin neman zabe domin tsaya wa takara a zaben shugaban kasar da za a yi a shekarar 2018.
Labaran da jaridun kasar suka fitar na cewa, Mugabe ya yi jawabi a ofishin jam’iyyar Zanu PF a Harare babban birnin kasar inda ya ce, ya fara kamfe din sake tsaya wa takara a zaben daza a yi a shekara mai zuwa.
Ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki don ganin ‘yan asalin Afirka kuma bakaken fata sun fi mallakar kasa a Zimbabwe.
Mugabe ne shugaban kasa a nahiyar Afirka da ya fi kowanne tsufa.
Ya kuma ce, baya ga shi bai ga wani dan takara da ya dace da kasarsa ba.