Mugabe zai gana da shugaban sojoji  ranar Lahadi


Shugaban kasar Zimbabwe,Robert Mugabe,ya shirya ganawa da shugaban rundunar sojin kasar a ranar Lahadi karo na biyu kenan da mutanen za su gana cikin mako guda.

A cewar gidan talabijin na ƙasar ZTV ya jiwo babban limamin kirista, Fidelis Mukonori  dake shiga tsakani yana fadar ganawar da aka shirya yinta ranar Lahadi.
A kuma ranar ne jami’iyar ZANU-PF zata gudanar da taronta inda ake sa ran za ta kori Mugabe daga matsayin sa na jagoran jam’iyar.

Ana kuma sa ran jam’iyar zata dawo da tsohon mataimakin shugaban kasa da aka kora, Emmerson Mnangagwa,wanda sojoji suke goyon baya a matsayin mataimakin shugaban jami’iyar.

Haka kuma ana sa ran jam’iyar zata cire Grace Mugabe, daga mukaminta na  shugabar matan jam’iyar.

Hakan na zuwa ne dai dai lokacin da ake gudanar da zanga-zangar neman Mugabe yayi murabus.

You may also like