Muhawara kan sayarwa Saudiyya makamai


 

 

Yau ne majalisar dattawan Amirka za ta yi zama kan batun sayarwa Saudiyya da makamai wanda kudinsu ya haura dala miliyan dubu daya batun da ya jawo rabuwar kai a majalisar.

018217369_30300

 

 

Masu aiko da rahotanni suka ce wannan batu na sayarwa Saudiyya makaman na shan suka sai dai jagoran ‘yan majalisar na bangaren jam’iyyar adawa ta Republican Mitch McConnell ya ce zai yi dukkanin mai yiwuwa wajen ganin an yi watsi da wannan kuduri na hana sayarwa Saudiyya din makamai.

To sai dai a daura da wannan wasu ‘yan jam’yyarta Republican da kuma takwarorinsu na Demokrat da ke mulki sun ce za su yi bakin kokarinsu wajen ganin an yi watsi da wannan kuduri duba da abinda suka ce Saudiyya din na yi a kasar Yemen.

A farkon watan jiya ne ma’aikatar tsaron Amirka ta Pentagon ta sanar da batun sayarwa Saudiyya din da makamai wanda suka hada da tankokin yaki 130 da motoci masu sulke 20 da kuma sauran kayan yaki dama.

You may also like