
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un yana yi wa sojoji jawabi
Shekara da shekaru, Koriya ta Arewa ta kasance ɗaya daga cikin ƙasashe masu matuƙar sirri, da wuya a san halin da ake ciki a ƙasar.
Ta kasance ɗaya daga cikin tsirarun ƙasashen da suka rage ƙarƙashin mulkin kwamunisanci.
Burin ƙasar na bunƙasa ƙera makaman nukiliya ya sanya ƙasar zama saniyar ware a tsakanin ƙasashen duniya.
Ƙasar ta yunƙuro ne a shekarar 1948 daga rikita-rikita da kun-ji-kun-jin da suka biyo bayan Yaƙin Duniya na Biyu.
Tarihin ƙasar ba zai taɓa kammala ba, ba tare da an ambato jajirtaccen shugaban Koriya ta Arewa Kim Il-sung, wanda shi ya saisaita da samar wa siyasar ƙasar wurin zama tsawon kimanin shekara 50.
Gomman shekarun da aka ɗauka a kan wannan tsari ya sa mulkin ƙasar ya ta’allaƙa a kan fitattun mutane da ke cikin wani rukuni na masu ƙarfin faɗa-a-ji.
Hakan ya kuma ƙara zama dalilin da ake ganin tsarin da masu mulkin ƙasar suka ɓullo da shi na tafiya kafaɗa-da-kafaɗa da cin zarafi da take haƙƙoƙin ɗan adam.
Kim Jong-un shi ne shugaba na uku da ya mulki ƙasar daga daular Kim, wanda kakansa Kim il-Sung ya kafa.
Kim Jong-un ya gaji mulkin daga hannun mahaifinsa Kim Jong-il, tun yana raye daga bisani a watan Disambar 2011 ya rasu bayan ya yi fama da bugun zuciya.
Ƙarƙashin mulkin Kim Jong-un, Koriya ta Arewa ta ci gaba da yaɗa manufar da ya gada daga kaka da mahaifinsa, ta fuskar bunƙasa harkoki soji a cikin gida, da aika wa ƙasashen duniya saƙo ko tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro a kan shirin Koriya ta Arewa na makaman nukiliya.
Kafofin yaɗa labarai
Asalin hoton, Getty Images
Ana zargin gwamnati ta mai da ‘yan ƙasar ba a bakin komai ba, ta hanyar tsauraran matakai ga kafofin yaɗa labarai da wallafa abin da suke son a sani
Tashoshin Rediyo da Talbijin suna ƙarƙashin ikon gwamnati, kullum babu abin da suke yaɗawa sai farfaganda.
Ma’aikatan yaɗa labarai, ba su da kataɓus saboda akwai hukuma sukutum da gwamnati ta kafa mai bibiyar duk abin da suke yi, da zarar sun ga wani abu na suka ga Shugaba Kim, to matakin da za a ɗauka ba mai kyau ba ne.
Koriya ta Arewa dai na fama da matsin tattalin arziƙi, da mummunan fari, amma ko sau ɗaya ba a taɓa ji wani abu makamancin haka a kafofin yaɗa labaran ƙasar ba.
Ƙasar na cikin ƙasashen da aikin jarida ke da matuƙar wuya a duniya.
Muhimman Lokuta
Bayanai kan muhimman abubuwan da suka faru a tarihin Koriya ta Arewa:
1945 – A shekarar ne aka kawo ƙarshen mulkin mallakar Japan, tare da miƙa wuya a ƙarshen Yaƙin Duniya na Biyu.
1948 – An raba Koriya gida biyu, inda Tarayyar Sobiyet ke mara wa Arewa baya, Amurka kuwa na mara baya ga Kudu.
1950-1953 – Yaƙin Koriya ya zo ƙarshe bayan sasantawa.
1994 – Shugaba Kim Il-sung da ya kafa ƙasar ya rasu, daga nan sai ɗansa Kim Jong-il ya gaje shi, kafin rasuwarsa shi ma a 2011.
2018 – Kim Jong-un ya zama shugaban Koriya ta Arewa na farko da ya shiga Koriya ta Kudu domin ganawa da shugaban Kudun Moon Jae-in.
Makwanni bayan nan, ya kuma gana da shugaban Amurka na lokacin Donald Trump.
Asalin hoton, Getty Images
Sojin ruwan Amurka sun tusa ƙeyar ‘yan Koriya ta Arewa a matsayin fursunonin yaƙi lokacin yaƙin Koriya, wanda China ta mara wa Arewa baya da yin watsi da Kudu wadda ta samu goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya.