
Kwana goma cif a yi zaɓen shugaban kasa da na ‘yan majalisar dokoki ta tarayya, wadanda za a gudanar a ranar Asabar 25 ga wannan wata na Fabarairu.
Sannan a gudanar da zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalsar dokoki na jihohi a ranar 11 ga watan gobe na Maris.
Malaman addinai da masu fafutika da masana na jan hankalin ‘yan kasar kan muhimmnaci fita a kaɗa kuri’a.
Kan haka ne muka shirya kawo maku jerin rahotanni na musamman tun daga wannan Talatar a matsayin tunatarwa da kuma gyara kayanka.
‘Abin da ya kamata a sani’
Fitar jama’a su je rumfunan zaɓe, su kaɗa kuri’a kamar yadda Marigayi Mammalon Shata ya nusar, wani muhimmin abu ne “mai tangan da babban ɗan yatsa”, wanda ‘yan iya magana kan ce, ‘in babu shi, ba kaɗi ba yanta’.
Barista Muhammad Mansur, malami a jami’ar Usmanu Dan Fodio da ke Sakkwato, ya kalli abin ta fuskar kundin tsarin mulkin Najeriya.
Ya shaidawa BBC cewa sashi na 77 na kudin tsarin mulkin kasa ya tanadi duk wani ɗan Najeriya wanda ke zaune a kasar kuma ya kai shekara 18 a yi masa rajista ya yi zaɓe.
Zaɗe ƴanci ne ga yyan kasa duk bayan shekara hudu ya zaɓi wanda yake so, idan mutum bai yi masa ba sai ya sauya su.
‘Zaɓi sonka’
Shi kuwa Dokta Kole Shettima, shugaban cibiyar tabbatar da dimokuradiyya da raya kasa, wato CDD, a Najeriya, ya ce yin zaɓe wata dama ce irin ta zaɓi sonka ga ‘yan kasa.
Ya ce ƴanci ɗan adama ne mutum ya zaɓi wanda zai shugabance shi, ba wai mutum ya ɗau bindiga ya ce zai mulki mutum ba.
Don haka yana da muhimmanci mutane su fito su kaɗa kuri’arsu domin samun mutumin da zai shugabance su cikin adalci.
Kuma mutum na da dama bayan wasu shekaru idan bai gamsu ba, ko bai cika burinsu ba, ya sake zaɓen wani mutum ko shugaba na gaba.
Ba dai-dai ba ne mutum ya noƙe ko yaƙi fitowa a ranar zaɓe.
‘Kuri’arka ‘yancinka’
Shi kuwa Farfesa Ibrahim Ahmad Makari, limami daga cikin limaman babban masallaci na kasa da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, ya ce yin zaɓe wani wajibce ne.
Ya ce ta hanyar fitowa a yi zaɓe ne kawai za a iya tabbatar da adalci a bayan kasa.
Kuma wajibi ne mutum ya yi iya kokari wajen bada gudumawarsa, cikin tabbatar da adalci domin kuri’arka ɗaya na iya ba da bambanci, mutum ya samu daukaka kan wani.
Zaɓe na da kyakyawan tasiri a ciki al’umma.
‘Zabe wani abu ne mai dadadden asali’
Rabaran Murtala Mati Dangora, wani jigo a kungiyar Kiristoci ta Najeriya, wato CAN, ya ce yin zaɓe wani abu ne mai dadadden asali.
“Zaɓe ba sabon abu ba ne a cikin littafi mai tsarki, saboda sarki Isra’ila na farko jama’a ne suka fito suka zabe shi lokacin Annabi Isma’il”, in ji Mati Dangora.
“Sannan lokacin salwantar ɗaya daga cikin almajirin Yesu, zaɓe sauran almajirai suka kira domin maye gurbinsa.”
Ya ci gaba da cewa, Zaɓe wajibi ne domin bai wa mutane da suka dace damar mulki.
Zaɓe ‘yancin ‘yan kasa ne don haka dole kowa ya fita ya kada kuri’arsa.
Mutane su daina tunanin cewa kuri’arsu ba za ta yi tasiri ba, domin ‘yancinsu ne da ke iya kawo sauyin da ba su taɓa tunani ba.
Yanzu dai hankali ya koma ne ga batun yadda fitowar jama’a za ta kasance a zabukan da ke tafe, wadanda galibi ake yi wa kallon mace da ciki, wadda ba a san abin da za ta haifa ba.