
Janairu – Shekarar 2022 ta fara bude shafinta a arewacin Najeriya da hare-hare inda tun daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Janairun sabuwar shekarar ‘yan bindiga haye a babura kimanin 300 suka kai hari wasu garuruwa guda biyu na Kurfar Danya da Rafin-Gero a kananan hukumomin Anka da Bukkuyum.
Sun kashe mutum kimanin 200, bayan bude wuta irin ta kan mai uwa da wabi tare da kona gidaje da abinci da dabbobi.
Janairu – Da yammacin ranar 14 ga watan Janairu ne dai har wayau ‘yan bindiga suka kashe mutum akalla 50 a kauyen DanKade da ke jihar Kebbi, bayan sun kone rumbunan garin sannan sun yi artabu da jami’an tsaro inda suka kashe dan sanda da soja.
Fabrairu – A watan Fabrairu ne kungiyar malaman jami’a ta ASUU ta tsunduma cikin yajin aikin bisa neman martaba wasu jerin yarjejeniyoyi da ta yi da gwamnatin tarayya a shekarun baya.
Dubban daliban jami’o’i a Najeriyar dai sun kwashe watanni kimanin takwas a suna zaman gida har zuwa watan Oktoba lokacin da kungiyar ta ASUU ta janye yajin aikin bayan wani umarnin kotun daukaka kara.
Asalin hoton, Getty Images
Maris – Haka aka yi ta samun matsalar tsaro can da nan har zuwa ranar 28 ga watan Maris, inda wani harin da kungiyar Boko Haram ta kai kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ya yi sanadin mutuwar da jikkatar gomman fasinjoji sannan kuma aka yi garkuwa da fiye da 60.
Jirgin dai ya tashi ne daga Idu – daya daga cikin tashoshin jirgin kasa na Abuja zuwa Rigasa da ke Kaduna.
Kuma bayan isarsa kauyen Katari ne sai ‚yan bindigar suke dasa bama-bamai har guda biyu kafin ya tsaya su bude wuta a kan jirgin.
Kuma tun wannan lokacin ba a kara jin duriyarsu ba har sai bayan kimanin mako biyu.
A karon farko, ‘yan bindigar da suka yi jawabi, inda suka yi barazanar kashe fasinjojin da suka sace matuƙar gwamnatin Najeriya ba ta biya musu buƙatunsu ba.
Kuma tun daga wannan lokaci suka rinka sakin bidiyo mai dauke da yadda suke ‘yan bindigar ke lakada wa fasinjojin duka yayin da su kuma suke ta kuka da kururuwa, duk da sun rinka sakin mutanen da suka sace da kadan-kadan.
Afrilu – A ranar 22 ga watan Afrilun shekarar ta 2022 ne wata fashewar bututun mai sakamakon dibarsa da ake ba bisa ka’ida ba ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye 110 a wani gari da ke kann iyakar jihar Imo da Rivers.
Mayu – A ranar 12 ga watan Mayu ne kuma wata tarzoma ta so ta kunno kai tsakanin ‘yan Najeriya bayan wani kisan a tara-a-tara da wasu matasa suka yi wa wata daliba mai suna Deborah bisa zargin batanci ga Annabi Muhammad SAW.
Mayu – A ranar 28 ga watan Mayun dai ne mutum 31 suka mutu sannan bakwai suka jikkata sakamakon turereniya a wajen karbar abincin sadaka a wata coci a jihar Rivers.
Mayu – Bugu da kari, a watan na Mayu ne wasu ‘yan bindiga suka dąsa dan ba na kai hare-hare kan ofisoshin hukumar zabe, a kananan hukumomin Ezza North da Izza da ke jihar Ebonyi a kudu maso gabshin Najeriya. An dai fi alakanta harin da aikin ‚yan kungiyar IPOB masu son kafa kasar Biafra.
Mayu – Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya zamo dan takarar shugabancin kasar a karkashin jam’iyyar adawa ta PDP, a ranar 28 ga watan na Mayu. Alhaji Atiku Abubakar ya lashe zaben ne da kuri’a 371.
Yuni – Shi kuwa dan takarar shugabancin kasar na jam’iyya mai mulki ta APC, Bola Ahmed Tinubu ya zamo dan takarar jam’iyyar ne a ranar 8 ga watan Yuni bayan kayar da sauran abokan takararsa guda 13.
Yuni – Har wa yau a ranar 5 ga watan na Mayu ne kuma wasu ‘yan bindiga sun bude wuta kann masu bauta a wata coci da ke garin Owo na jihar Ondo inda suka kashe masu ibada fiye da 40.
An dai ta kaiwa da komowa dangane da hakikanin maharan, inda aka ce ‚yan kungiyar ISWAP ne masu ikrarin jihadi.
Yuli – A watan Yuli ne ‘yan Najeriya suka cika da mamaki bayan da wani bidiyo ya fita dauke da barazanar da ‘yan ISWAP wadanda suka kai hari kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna suka yi ta sace shugaba Buhari da gwamnan jihar kaduna, Malam Nasir Elrufa’i.
Yuli – To sai dai harin da wasu ‘yan bindiga suka kai gidan yarin Kuje da ke Abuja ya jefa ‚yan Najeriya cikin rudu kasancewar faruwar al’amarin a kewayen babban birnin tarayya.
An dai ce mahara ne dauke da muggan makamai hadi da bama-bamai suka kutsa cikin gidan yarin bayan yin nasara a kann ma’ikata, inda kuma suka saki jama’arsu sannan sauran tsararru kowa ya yi ta-kansa.
Alklauma daga ministan cikin gida na Najeriya sun nuna akalla mutum fiye da 800 ne suka arce a lokacin kuma ciki har da ‚yan Boko Haram guda 60.
Yuli – Idan dai ba a manta ba, a watan na Yuli ne Wata babbar kotu a jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yanke hukuncin kisa ga Abdulmalik Tanko kan samun sa da laifin kashe dalibarsa mai suna Hanifa Abubakar.
Yuli – Tun dai a watan na Yuli ne al’umma a sassa daban-daban na Najeriya suka fara fuskantar ambaliyar ruwa da masana suka ce ba su taba ganin irinta ba a baya-bayan nan.
Ambaliyar ta kuma dangane har zuwa watan Satumba, inda alkaluma suka nuna cewa akalla mutum miliyan 1.3 ne suka rasa matsugansu sannan mutum fiye da 600 suka mutu, baya ga kusan 2500 da suka jikkata.
Kimanin gidaje dubu 82 ne suka lalace sannan hecter fiye da dubu 300 ruwan ya share.
Asalin hoton, Getty Images
Satumba – Sakamakon ambaliyar a watan na Satumba, ‘yan Najeriya suka fara fuskantar dogwayen layuka a gidajen mai bisa mamayar da ruwan ya yi wa Lokoja na jihar Kogi wata hanya daya tilo da ta hada kudanci da arewancin kasar.
To sai dai duk da cewa ruwan ya janye amma har zuwa yanzu a watan Disamba, ‚yan Najeriya na dandana kudarsu a gidajen mai musamman a garuruwan da Legas da Abuja ba.
Satumba – A watan Satumbar ne al’ummar birnin Kano suka wayi gari da labarin cewa ƴan sanda sun kama wani mutum ɗan ƙasar China bisa zarginsa da kashe wata budurwarsa a Jihar Kano da ke arewacin ƙasar. Har kawo yanzu dai ana wannan shari’a ba ta kare ba.
Oktoba – A watan Oktoba ne kuma aka saki ragowar fasinjojin jirgin Abuja zuwa Kaduna da ‚yan bindiga suka hara a watan Maris, bayan sasantawa da gwamnati.
To sai dai iyaye da ‚yan uwan fasinjojin sun ce sai da suka biya makudan kudi kafin a sakar musu ‚yan uwan nasu.
Oktoba – Ana tsakan da wannan murna sai Kotun daukaka ƙara ta Najeriya ta kori ƙarar gwamnati tarayya a kan jagoran ƙungiyar ƴan aware ta IPOB Nnamdi Kanu, ta hanyar yin watsi da dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa.
Tawagar alkalan ta mutum uku da Mai Shari’a Jummai Hanatu ta jagoranta ta ce Kanu ba shi da laifin amsawa saboda tun farko Babbar Kotu ba ta da hurumin yi masa shari’a tun farko.
Hukuncin kotun ya ce matakin kamo Kanu da aka yi da dawo da shi Najeriya daga Kenya ya kauce wa doka. Alkalan sun ce an dawo da shi Najeriya ne ba bisa ƙa’ida ba.
To sai dai gwamnatin Najeriya ta ce ta daukaka kara kan batun.
Disamba – Da yammacin ranar 1 ga watan Disamba ne uwar gidan shugaban Najeriya, Hajiya Aisha Buhari ta bakin lauyanta ta janye tuhumar da take yi wa dalibin jami’ar Dutsen nan, Aminu Muhammad wanda aka zarga da cin zarafinta a kafar twitter.
Disamba – A ranar Alhamis 15 ga watan na Disamba ne kuma wata babbar Kotun Shari’ar Musulunci a Jihar Kano ta yanke wa Sheikh Abduljabar Nasiru Kabara hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samun sa da laifi yin kalaman rashin tarbiyya ga Annabi Muhammad.
To sai dai malamin ya musanta laifin nasa inda ya ce ba ya neman sassaucin kotun.
An dai bai wa Abduljabbar kwanaki 30 ya daukaka kara.