
Kamar kowacce shekara, mazauna duniyarmu ta Az sun fuskanci abubuwa daban-daban a 2022, wasu na tarihi, wasu kuma ci gaba ne daga 2021.
Wannan muƙala ta duba muhimmai a cikinsu – kamar yaƙin Ukraine, da Gasar cin Kofin Duniya, mutuwar Sarauniyar Ingila, ƙarin yawan al’umma.
Janairu – murka ta karya da mutum million 1.34 na adadin waɗanda suka kamu da cutar korona nau’in Omicron a watan Janairun 2022.
Janairu – A dai watan na Janairu ne Fadar Buchinham ta Ingila ta tube wa Yarima Andrew mukaminsa na soja da sarautarsa kwana daya bayan da wata kotu ta amince da ci gaba da shari’ar da ake yi masa kan zargin da Virginia Giuffre ta yi na tilasta mata da ta ce an domin saduwa da Yariman a lokacin tana shekara 17.
Janairu – A karshen watan na Janairu ne kuma sojoji A kasar Burkina Faso karkashin ikon Lt-Col Paul-Henri Sandaogo Damiba suka kifar da gwamnatin shugaba Roch Kaboré bisa dalilin da suka bayar da gazawarsa wajen yakar mayaka masu ikrarin jihadi a kasar.
Asalin hoton, RTB
Kanar Damiba ne ya jagoranci juyin mulkin
Fabarairu – Idan dai ba a manta ba, a ranar 24 ga watan Fabrairu ne sojojin kasar Russia suka kutsa cikin Ukraine a ci gaba da zaman tankiyar da ya fara tun shekarar 2014.
Alkaluma daga ofishin hukumar ‘yan gudun hijra ta majalisar dinkin duniya sun nuna cewa ya zuwa ranar 18 ga watan nan na Disamba, akalla yakin ya tilasta fiye da mutum miliyan 32 yin gudun hijra, sannan fiye da mutum miliyan 6 sun mutu.
Asalin hoton, Reuters
Watannin kuma da suka biyo bayan yakin na Russia da Ukraine har kawo yanzu sun bullo da tsadar makamashi musamman iskar gas da wutar lantarki, al’amarin da ya kuma shafi sauran fannonin rayuwa.
Afrilu – Al’ummar kasar Afirka ta Kudu bas u ji dadin watan Afrilu ba sakamakon mutuwar mutum kusan 500 saboda ambaliar ruwa da zabtarewar kasa a yankin Kwazulu Nataal na kasar ta fuskanta.
Mayu – Idan muka koma batun yakin Russia da Ukraine, shi ne ya kankane taron tattalin arziki na duniya da aka yi a watan Mayu a Davos na kasar Switzerland, inda Kwararru da masana harkar tattalin arziki fiye da 2000 daga ko’ina a fadin duniya suka halarta.
Karin batutuwan da aka tattauna a yayin taron sun hada makomar tattalin arzikin duniya tun bayan ficewa daga annobar korona da batun dunkulewar duniya wuri guda da matsalar abinci da makamashi da kuma sauyin yanayi.
Yuli – Ranar 7 ga watan Yulin shekarar 2022 al’ummar Burtaniya suka wayi gari da murabus din firaministansu, Boris Johnson da ya kawo karshen mulkinsa mai cike da takaddama na shekara uku. Kuma bayansa ne wasu Karin firai ministocin guda biyu su ma suka yi ta yin murabus.
Yuli da Yuni – A watannin Yuni da Yuli ne duniya ta fuskanci zafin da za a iya cewa ba ta taba ganin irinsa ba.
Asalin hoton, Getty Images
Nahiyoyin Turai da Afirka ta Arewa da yankin Gabas ta Tsakiya da Asiya duk sun fuskanci zafin da ya haura maki 40 a ma’aunin Celcius.
Wannan al.’amri dai ya haddasa wutar daji a dazuka da garuruwa daban-daban. Alkaluma sun nuna akalla mutum kusan 250 ne suka mutu sannan kimanin 200 suka jikkata sakamokn zafin mai tsanani da duniya ta fuskanta. Zafin ya kuma yi sanadiyyar afkuwar fari a kasashen turai masu dausayi.
Yuni – Agusta – A watannin Yuli da Agusta, kasar Pakistan ta fuskanci wata irin ambaliya mai kama da Tsunami da ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 1,391, sannan ta janyo asarar muhalli da kayan amfanin gona da kayan more rayuwa na kimanin dala biliyan 30.
Satumba – A ranar 16 ga watan Satumba ne wasu ‘yan kasar Iran suka fara hawa tituna suna zanga-zangar yin Allah-wadai da kisan da ‘yan sandan Hizba suka yi wa Mahsa Amin wadda suka tuhuma da rashin lullubi.
Asalin hoton, Twitter
Wata mai zanga-zanga a Iran
Zanga-zangar ta yi ƙamarin da har yanzu ba a iya zuba mata ruwa ba. Alkaluma masu karo da juna ke nuna cewa jami’an tsaro sun yi sanadiyyar mutuwar masu zanga-zanga 450.
To sai dai hukumomin kasar Iran na alakanta alkaluman da farfagandar yammaci.
Satumba – A watan Satumba ne shugaban Hukumar Lafiya Ta Duniya, Dr Tedros Adhanom Gebreyesus yayi wata bushara da zuwan karshen annobar korona ta kunno kai a 2020 wadda ko da a shekarar nan mai shudewa sai da aka samu rasuwar mutane kimanin miliyan daya.
“Ya ce alkaluman da muka samu a makon da ya gabata na wadanda suka mutu sakamakon annobar korona, su ne suka fi kowadanne karanci tun watan Maris din shekarar 2020. Wannan ne lokacin da ya fi kowanne wajen kawo karshen annobar. Duk da cewa har yanzu da sauran rina a kaba, amma muna dab da dakile ta. Muna samun nasara a kanta.”
Oktoba – A can kuwa Seuol babban birnin kasar Korea ta Kudu mutum fiye da 140 ne suka mutu sannan gommai suka jikkata a ranar Asabar ta 29 ga watan Octoba sakamkon turmutsutsi a yayin wani bikin al’ada na Holloween.
Nuwamba – A ranar 2 ga watan Nuwamba ne gwamnatin kasar Ethiopia da kungiyar neman ‘yancin Tigray suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya wadda ta kawo karshen zaman tankiyar da bangarorin biyu suka kwashe shekaru biyu suna yi.
Nuwamba – Ranar 15 ga watan Nuwamban 2022 ne duniya ta bude sabon babin tarihi na yawan jama’a inda yawan al’ummar duniyar ya kai biliyan 8 cif-cif.
Nuwamba – Har wa yau, a watan na Nuwamba ne masana da kwararru fiye da dubu 35 suka hadu a wurin shakatawa na Sham el-sheikh da ke kasar Egypt domin tattaunawa kan batun sauyin yanayi. Na kira taron da COP27 kuma bayan kammala taron an cimma kudirin samar da gidauniyar da za a yi amfani da kudin domin kashe kaifin asara sakamakon ibtila’i.
Nuwamba – A ranar 20 ga watan Nuwamban shekarar nan mai shudewa ne aka take kwallon farko tsakanin Qatar mai masaukin baki da Equador a gasar kwallon kafa ta duniya irinta ta farko a kasashen Labarabawa kuma Musulmi.
Disamba – Kuma a ranar 18 ga watan Disamba ne kasar Argentina ta lashe kambun bayan buge Fransa da ci 4-2 a bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Asalin hoton, Getty Images
Messi ne ya jagoranci tawagar Argentina ta lashe kofin karo na uku a tarihi
Disamba – Kwana 12 kacal da lashe kofin ne kuma, ranar 29 ga wata tauraron ɗan ƙwallon Brazil, Pele, ya rasu sakamakon cutar daji wato kansa da ya sha fama da ita.
Asalin hoton, Getty Images
Pele ya lashe Gasar Kofin Duniya sau uku – mafi yawa a tarihi
Ya rasu a ƙasarsa yana da shekara 82 bayan lashe Gasar Kofin Duniya uku – mafi yawa a tarihi ga wani ɗan wasa ya zuwa yanzu.