Muhimman Matakai 7 da Gwamnatin Tarayya Zata Dauka A Shekarar 2018A cikin jawabin sa ya gabatar da kafafen yadda labarai albarkacin sabuwar shekarar 2018, shugaban kasa Muhammadu Buhari bayyana wasu muhimman matakai da gwamnatin sa take shirin dauka, domin bunkasa cigaban tattalin arzikin kasa da walwalar ‘yan Nijeriya. 

Daga cikin matakan da abubuwan da jawabin na shugaban kasa ya fi mayar da hankali a kansu, har da:

  • Hana shigo da shinkafa daga kasashen waje, domin bunkasa noman ta gida da farfado da manoman shinkafa. 
  •  Gwamnati za ta bunkasa sufuri ta hanyar samar da layukan dogo da kuma inganta hanyoyin mota.
  •  Za a sake inganta wutar lantarki ta hanyar kara tashoshin samar da wuta da bunkasa hanyoyin rarrabata.
  •  Gwamnati ta murkushe Boko Haram kuma za ta magance masu garkuwa da mutane nan bada jimawa ba.
  • Ya kamata matasa su samawa kansu ayyukan yi maimakon neman aiki a gwamnati ko kamfanoni masu zaman kansu.
  • Babu bukatar sake fasalin tsarkin mulkin Nijeriya, sai dai a mayar da hankali wurin aiwatar da shi bisa ka’ida.
  •  Babu ruwan siyasa da addini ko kabilanci, don haka ya kamata ‘yan Nijeriya su yi koyi da Yarabawa, wadanda su ba sa bari bambancin addini da siyasa su yi tasiri a siyasarsu.

You may also like