
Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist (Multimedia)
- Twitter,
Azumi dai farilla ne cikin rukunnan Musulunci, wanda Allah ya shar’anta wa duk wani Musulmi baligi.
Azumi na nufin mutum ya kame bakinsa daga ci da sha da kuma saduwar iyali tun daga Alfijir har zuwa faɗuwar rana.
Yana cikin ginshiƙan ibadu da Musulmi ke yi tsakaninsu da Allah, ba wai kawai don neman lada ba, domin azumi yana taimakawa wajen inganta imanin Musulmai tare da kyautata halayensu.
Abin so ne ga kowane Musulmi ya yi buɗa-baki da zarar rana ta faɗi ko kuma an yi kiran sallar Magariba.
BBC ta tuntuɓi malamai domin samun ƙarin haske game da buɗa-baki da kuma abubuwan da suka kamata mai buɗa-baki ya siffantu da su.
Mallam Mustapha Usman Ahmad, babban malami na Madabo kuma limamin masallacin Juma’a na Abdullahi Bn Abbas a Kano ya ce yin buɗa baki yana tattare da falala mai yawa musamman idan an yi a kan lokaci.
Ya jingina hakan ga hadisin sahabin Manzon Allah (SAW) Abu Hurayra kamar haka “cikin hadisan da Manzon Allah ke ruwaitowa daga Ubangijinsa, Manzon Allah ya ce shi mai azumi yana da farin ciki guda biyu – lokacin da zai yi buɗa baki da yin buɗa-baki a lokacinsa.”
A cewarsa, mutumin da ya yi buɗa baki, ya dace da sunnar manzannin da Allah (SWA) ya aiko domin su ma suna yin azumi kuma suna yin buɗa-baki.
Dr Ali Yunus, Babban Limamin Uthman Bn Affan da ke Gadon Ƙaya a birnin Kano ya bayyana cewa yin buɗa-baki na da matuƙar muhimmanci kasancewar idan rana ta faɗi to azumi ya ƙare “ko da mutum bai ci abinci ba.”
Ya ce akwai alheri mai yawa a yin buɗa baki kuma Allah Yana son bayinSa masu buɗa baki kamar yadda ya zo a cikin hadisin Imamu Tirmidhi.
Illar Jinkirta shan ruwa…
Mallam Mustapha Usman ya ce duk mai jinkirta buɗa-baki yana rasa alheri mai girma.
“Ɗabi’ar annabawan Allah, dukkansu suna yin azumi, suna jinkirta yin sahur suna kuma yin gaggawa wajen shan ruwa.”
Annabi ma ya ce, “mutane ba za su gushe cikin alkhairi ba, matuƙar suna gaggauta buɗa-baki – wanda ya ke gaggauta shan ruwa zai dace da alkhairin da Annabi ya ambata.”
Malamin ya kuma ce jinkirta shan ruwan yana nufin mutum ya haɗu da illa ta rashin samun dace da abin da Annabawa da Manzanni suka tafi a kansa.
A nasa ɓangaren, Dr Ali Yunus ya ce jinkirta yin buɗa-baki ya saɓa wa sunnar Manzon Allah (SAW).
“Ba daidai ba ne mutum rana ta faɗi yana mai azumi kuma ya ƙi sa wani abu a bakinsa ya yi buɗa baki, wannan kuskure ne.” in ji Dr Yunus.
Ya kuma ce buɗa baki da gaggawa yana ƙara wa mutum kuzari da zai yi sallar ƙiyamul layli bayan ya ajiye azuminsa musamman idan mutum ya kiyaye ƙa’idojin da shari’a ta faɗa – ya kasa cikinsa gida uku: gida ɗaya ya ci abinci, gida ɗaya ya sha ruwa sannan kashi na uku kuma ya bari don numfasawa.
Game da mai azumin da ya ƙi yin buɗa baki kuwa, Dr Ali Yunus, ya ce babu wani laifi idan mutum ya yi azumi amma ya ƙi buɗa baki – azuminsa ya inganta.
“Amma ya saɓa wa sunnar Annabi, kuma Manzon Allah ya hana zarcewa da azumi ba tare da yin buɗa baki ba.” in ji shi.
Me ya kamata mai azumi ya siffantu da su yayin ajiye azumi?
Mallam Mustapha ya ce akwai buƙatar duk mutumin da zai yi buɗa baki ya siffantu da yanayin da Annabi Muhammad yake siffantuwa da su a lokacin da zai yi buɗa baki.
Ya ce ana so mai buɗa baki ya siffantu da yin amfani da kayan marmari masu ruwa-ruwa a lokacin da yake buɗa baki.
“Idan mutum bai samu wannan ba, sai ya yi amfani da dabino, idan bai samu dabino ba, sai ya yi amfani da ruwa,” in ji Babban Malamin na Madabo.
A cewarsa, “abin da zai tabbatar mana da wannan shi ne hadisin Nana Aisha da ta ce Manzon Allah SAW ya kasance yana yin buɗa baki da ƴaƴan itatuwa masu ruwa-ruwa, idan bai samu ba yana amfani da dabino, idan bai samu dabino ba, yana amfani da ruwa gwargwadon yadda zai ishe shi,”
“idan ruwan ma bai isar masa ba, Manzon Allah yana amfani da kowanne nau’in abinci wanda zai gamsar da shi, idan kuma bai samu duk waɗannan ba, sai ya yi niyyar buɗa baki, saboda muhimmancin buɗa bakin.
Dr Ali Yunus ya ƙara a kan abin da Babban Malami na Madabo ya ce game da yadda Manzon Allah (SAW ) yake buɗa baki. “Yana buɗa baki ne da dabino wutiri ma’ana guda uku ko guda bakwai.”
Ya kuma ce yana da muhimmanci mai azumi ya guji cika cikinsa a yayin shan ruwa ta yadda zai kasance cikin kasala da rauni ta yadda ba zai iya sallolin dare ba.
Yin addu’a yayin buɗa baki yana da falala mai yawa don haka yana da kyau mai azumi ya yi addu’a a lokacin buɗa baki.
Dr Ali Yunus ya ce addu’o’in da aka fi so a lokacin buɗa baki su ne na neman dukkan alkhairan duniya da lahira da kuma neman tsari daga dukkan abin da ake gudu na sharrin duniya da lahira.