Mukaddashin Shugaban Kasa Ya Ba Da Umarnin Ci Gaba Da Shirin N-Power Mukaddashin  Shugaban Kasa , Farfesa Yemi Osinbajo ya bayar da Umarnin sake bude shirin Gwamnatin Tarayya na N-Power a ranar 17 watan Yuni don bayar da damar samun ayyuka, da kuma kud’ad’en yin sana’o’in dogaro da kai ga matasa, mata da Yara.

Wannan jawabin dai ya fito ne daga bakin karamar ministar kasafi da tsare-tsare, Hajiys Zainab Ahmad kamar yadda ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, NAN a jiya. 

Tace, tun farko an samu tsaiko a shirin me domin a tsaftace shi daga rashin gaskiya da babakere.

Ta kuma kara da cewa, ak’alla ‘Yan Najeriya miliyan d’aya da dubu Dari shida ne suka amfana da shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya da suka had’a da N-Power, ciyar da dalibai, bayar da tallafin N5,000 ga mutane mafi talauci  da kuma Samar da jarin dogaro da kai.

You may also like