Mukaddashin Shugaban Kasa Yakai Ziyara Maiduguri Sa’o’i Kadan Bayan Harin  Boko Haram Yanzu haka mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo, na can a birnin Maiduguri,babban birnin jihar Borno don kaddamar da shirin musamman na tallafawa yan gudun hijira.

Osinbajo na ziyara a birnin ne sa’o’i  kadan  bayan da yan kungiyar Boko Haram suka kai hari a wasu unguwanni dake birnin inda suka kashe mutane da dama tare da kona gidaje masu yawa. 

A ranar Laraba jami’an tsaro sunyi musayar wuta da yan kungiyar ta Boko Haram tsawon  sa’o’i  da dama,duk da jami’an tsaro sun tabbatarwa da mazauna garin zasu kare lafiyarsu da yawa sun fice daga gidajensu. 

Mukaddashin Shugaban kasar ya ziyarci fadar shehun Borno, inda yace shugaban kasa Muhammad Buhari, ya damu da halin da yan gudun hijirar suke ciki. 

Karkashin Sabon shirin za’a rabawa yan gudun hijirar buhun hatsi bayan kowanne wata uku. 

You may also like