Muke Da Alhakin Tabarbarewar Tattalin arzikin Nigeria –  APC


Mu Ke Da Alhakin Tabarbarewar Tattalin Arzikin Nijeriya, Amma Mun Sha Alwashin Shawo Kan Matsalar, Inji Gwamnatin APC

Bayan tsawon watanni da ta dauka tana dorawa gwamnatin PDP alhakin tabarbarewar tattalin arzikin kasa, a karshe gwamnatin APC ta amince ita ke da alhakin hakan.
Haka kuma jam’iyyar mai mulki ta sha alwashin shawo kan matsalar
Jam’iyyar APC ta bayyana hakan ne ta bakin gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha wanda ya yi wa manema labarai bayani a yayin ganawar gwamnonin APC da shugaban kasa Muhammadu Buhari a Villa yau.

You may also like