Mummunan hatsarin jirgin kasa a Masar


 

Wani mummunan hatsarin jirgin sama ya afku a garin Giza na kasar Masar inda taragon jirgi guda 3 suka karye tare da kashe mutane 5 inda wasu 27 suka jikkata.

Jirgin na fasinjoji na kan hanyar Alkahira-Said inda ya fadi a lokacinda da yake sauya layi a garin Iyat wanda sakamakon haka taragonsa 3 suka fita daga jikinsa.

Ana bayyana yankin Iyat a matsayin yankinda aka fi samun hatsarin jirgin kasa a kasar Masar.

A shekarar 2002 jirgin kasa ya yi hatsari a wannan euri inda mutane 350 suka mutu.

A shekarar 2009 ma wasu jirage 2 sun yi taho mu gama a gurin inda mutane 30 suka mutu, wasu 60 kuma suka jikkata.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like