Mummunar gobara a sansanin ‘yan gudun hijirar Siriya


 

58609d84b5f4f

 

Jariri daya ya rasa ransa inda wasu mutanen 4 suka samu munanan raunuka sakamakon gobara da ta kama a sansanin ‘yan gudun hijira da ke yankin Azez na lardin Aleppon kasar Siriya.

Har yanzu ba a san me ya janyo gobarar ba wadda ta kama sansanin da ke kusa da kofar Öncüpınar ta iyakar Turkiyya da Siriya.

Gobarar ta jikkata wani mutum Abdulbahsi, matarsa Baran da kuma ‘ya’yansu Ravan, Nur da Maran.

duk kokarin da aka yi na ceton ran daya daga cikin yaron amma sai da ya rasa ransa.

An kai daya daga cikin wadanda suka jikkatan zuwa asibitin garin gazientep na Turkiyya.

You may also like