Mun Ƙi Sakin Liah Sharibu Ne Saboda Ta Ƙi Yadda Ta Ƙarbi Musulunci – BokoHaram


Har zuwa yanzu Boko Haram sun ki sakin Liah Sharibu daya daga cikin ‘yan matan Dapchi 110 da Boko Haram suka sace saboda ta ki amincewa ta karbi addinin musulunci.

Da farko dai gwamnatin tarayya ta bayuana cewa an sako 75 daga cikin ‘yan matan amma zuwa yanzu adadin wadanda aka sako ya karu 101.

Rahotanni sun nuna cewa tuni daliban suka tara da iyayen su, inda ita kuma Liah wadda take tsare a hannun ‘yan Boko Haram din suke ta kukan rashin dawowar ‘yar tasu.

You may also like