‘Mun fi kowa murnar kammala zabe’



Masu kada kuri'a

Asalin hoton, OTHER

A Najeriya, tuni wasu `yan takara da ke dakon a kammala zabensu suka yi maraba da sanarwar Hukumar Zabe mai Zaman Kanta ta kasar INEC, wadda ta sanya ranar 15 ga watan Afrilu mai zuwa don kammala zaben gwamnoni da na`yan majalisun dokoki a wasu sassan kasar.

Sanarwa INEC din ta kawo karshen dogon zaman jiran da al`umomin yankunan da zaben ya shafa da kuma `yan takara ke yi.

Jihar Adamawa da Kebbi su ne jihohi biyu rak da ba a kammala zaben gwamna ba a Najeriyar.

Tsohon ministan lafiya da harkokin wajen Najeriya kuma jigo a kwamitin yakin neman zaben gwamna Fintiri na jam’iyyar PDP a Adamawa, Dr Idi Hong, ya shaida wa BBC cewa, tsayar da ranar sake zaben za ta ba su damar sake shiri har su sake zuwa wuraren da aka soke zabensu don sake yada manufofinsu.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like