Mun kama yan shi’a 115 kuma babu wanda ya mutu yayin zanga-zangar – yan sanda


Rundunar yan sandan birnin tarayya Abuja ta ce ta kama yan shi’a 115 ya yin zanga-zangar da suka gudanar jiya a Abuja.Haka kuma ta musalta cewar daya daga cikin yan shi’ar ya rasa ransa a zanga-zangar da ta zama tashin hankali.

“Ba a samu asarar rayuka ba a zanga-zangar saboda jami’an yan sandan da aka tura sun nuna kwarewa wajen shawo kan lamarin,” a cewar Anjuguri Manzah mai magana da yawun rundunar yan sandan birnin.

Tun da farko Manzah ya shedawa jaridar The Cable cewa ba shi da masaniya akan arangamar da aka yi tsakanin ‘yan sanda da kuma yan shi’a.

A wata sanarwa da yafitar ranar Litinin bayan tashin hankalin da ya faru,mai magana da yawun rundunar ya ce masu zanga-zangar sun raunata jami’an yan sanda 22 suka kuma lalata kayayyaki yan sanda da na gwamnati.

Anjuguri ya ce kayan da aka samu a wurinsu sun hada da : Gwafa, karfe, duwatsu, danboris, da kuma dankwali ruwan hoda.

Ya ce masu zanga-zangar sun kuma kai hari kan mutanen da babu ruwansu, dagula al’amurran kasuwanci, kawo tsaiko ga zirga-zirgar ababen hawa da kuma fasa gilasan wasu motoci dake ajiye wuraren da zanga-zangar ta gudana.

You may also like