Mun kashe kakakin IS –  Amurka


Ma’aikatar tsaro ta Amurka ta ce hare-haren sama da Amurkar ta kai kan mayakan IS a Syria, a inda aka kashe daya daga cikin manyan shugabannin kungiyar, Adil Hasan Salman Fayad.
Mutumin wanda ake yi ma sa lakabi da ‘Dr Wa’il’, shi ne ministan yada labarai na kungiyar ta IS.

A karkashin Dr Wa’il ne dai ake samar da hotunan kisan da kungiyar take yi wa mutane.

Ma’aikatar tsaron dai ta ce an kai hare-haren ne a wani wuri kusa da Raqq, ranar 7 ga Satumba.

Shi dai Fayad ya kasance makusancin Abu Muhammad al-Adnani ne, mai tsare-tsare ga IS wanda kuma aka kashe yayin wani harin sama, a watan Yuli.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like