Mun Kashe Mutane Uku Akan Naira Dubu Tara Inji Wasu Barayin Babura A Jihar KatsinaWasu mutane biyu masu suna Umar Sada wanda aka fi sani da ‘Yaume’ da Ahmed Adamu wanda aka fi sani da ‘Dindingi’ wadanda dukkansu ke zama a yankin Kofar Sauri dake jihar Katsina, a jiya Litinin a ofishin ‘yan sanda sun bayyana yadda suka kashe wasu mutane uku tare da yin awon gaba da baburansu.

A yayin da yake yi wa manema labarai jawabi, Ahmed Adamu ya bayyana cewa ana biyan su naira dubu uku ne a duk mutum daya da suka kashe suka kwace masa babur.

“Bayan mun yi nasarar kwace babur din mukan dauki babur din mu kai Hirji wurin wani mai suna Mikailu Rahamawa wanda yake tsallakewa zuwa kasar Nijar kafin ya kawo mana kudin sallamar mu.

“A wasu lokutan akan biya mu naira dubu uku wani lokacin kuma naira dubu hudu, ya dai danganta da abin da mai sallamar zai fada mana, sai kuma mu koma bakin aiki, inji Ahmed.

Ya ce wadanda suka kashe su din, sun kashe su je a yankunan G.R.A., Lambum Danlwai da kuma Steel Rolling.
Shi kuma Umar Sada cewa ya yi “abinda nake so ga ‘yan sanda shine su shiga farautar duk wanda aka san suna da hannu a wannan harka ta satar babur, domin ni a nawa bangaren ina nadama”
“Mu kan yi amfani da kebul din babur ne wajen illata masu baburan daga bisani su mutu, mu kuma sai mu yi awon gaba da babur din.
A yayin da yake jawabi kan lamarin, kwamishinan ‘yan sandan jihar Katsina, Usman Abdullahi ya yi kira ga masu sana’ar tuka babur da su kiyayi daukar mutane zuwa yankunan da babu yawan jama’a. Ya kuma kara da cewa barayin baburan sukan sayar da babur ne kan naira dubu 15 zuwa dubu 40.
Ya kuma kara da cewa nan ba da jimawa ba za a maka wadanda ake zargin a kotu domin yi musu hukuncin da ya dace da su.

You may also like