Shugaban kungiyar Miyetti Allah na shiyar Arewa Ta Tsakiya, Alhaji Danladi Chiroma, ya ce akalla bafulatani guda ya rasa ransa ya yin da aka kashe shanu 53 mallakins yan tawagarsa a yankin Agatu dake jihar Benue.
Jaridar Daily Trust ta tabbatar da cewa yan sanda a makon da ya gabata sun tabbatar da mutuwar mutane a wani sabon hari da aka kai kan wasu garuruwa ciki har da Agatu.
Kwamishinan yan sandan jihar, Fatai Owoseni, a wani taron manema labarai jim kadan bayan ya gana da shugabannin kungiyar fulani a Makurdi ya ce wasu bata gari ne suka kashe biyu daga cikin mutane biyar din da suka mutu lokacin da suka kai hari a Agatu.
Amma Chiroma wanda ya yi magana da wakilin jaridar Daily Trust ya yi zargin cewa an kashe dabbobin ne ya yin wani hari da aka kai kan masu kiwon shanu dake Agatu kwanaki kadan da suka wuce, da wasu yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai.