Mun Shirya Zaman Sulhu –  Tsagerun Niger Delta 



Wasu kungiyoyin tsagerun Niger Delta guda hudu sun amince da tayin da Shugaba Muhammad Buhari ya yi masu kan su zo a zauna kan teburin sulhu don ganin an samu maslaha game da rikicin yankin.
Kungiyoyin sun cimma matsayin bayan wata tattaunawa da suka yi a birnin Port Hacourt na jihar Rivers inda suka yaba wa Shugaba. Buhari bisa wannan sabon yunkuri na neman samar da zaman lafiya a yankin.
A ranar Kirismeti ne dai a lokacin wata ziyara da kungiyar Kiristocin na Abuja suka kai masa a fadarsa, Shugaba Buhari ya roki mayakan tsagerun Niger Delta kan su ajiye makamansu don a samu damar yin zaman sulhu game da yadda za a raba arzikin man fetur da ake samu daga yankin.

You may also like