Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ibrahim Mantu, ya ce yana da hannu cikin magudin zabukan da aka yi a baya. Dan siyasar ya ce “ba dole ne sai na je rumfar zabe na sauya alkaluman zaben ba, amma mun bai wa jami’an hukumar zabe da jami’an tsaro kudi yadda idan sun ga wata dama da za su sauya sakamaon zabe domin ya taimaki jam’iyyarmu, sai su yi hakan.”
Sanata Mantu, wanda ya bayyana hakan a hirarsa da gidan talabijin na Channels TV, ya ce ya tuba daga aikata magudin zabe shi ya sa yanzu ya bayyana abubuwan da suka wakana a baya.
Tsohon dan majalisar dattawan fitaccen dan jam’iyyar PDP wanda a lokuta da dama aka zarge shi da hannu wajen cuwa-cuwar siyasa, ciki har da zargin yunkurin sauya kundin tsarin mulkin Najeriya ta yadda zai bai wa tsohon shugaban kasar, Cif Olusegun Obasanjo damar yin ta-zarce a karo na uku.