Mun Yi wa SamBo Dasuki Tayin Halartar Jana’izar Mahaifinsa – Danbazau


Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdurahman Danbazau ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ta bai tsohon mai ba Shugaban kasa shawara kan tsaro, Sambo Dasuki damar halartar Jana’izar mahaifinsa, Marigayi Ibrahim Dasuki amma ya ki amincewa da yin haka.
Danbazau ya nuna cewa tun lokacin da marigayin ke jinya an nemi Sambo Dasuki ya ziyarce shi amma ya nuna cewa zai ci gaba da yi masa addu’a daga inda ake ci gaba da tsare shi.

You may also like