Muna Bin Ka’idojin Kasa Da Kasa Wajen Kula Da ‘Yan Gudun Hijira – Buhari Shugaban Kasa, Muhammad Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa na bin ka’idojin kasa da kasa wajen kula da milyoyin ‘yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya shafa a jihohin Borno, Adamawa da Yobe.
Buhari ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da ya sadu da Babban Jami’in kula da ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya, Mista Phillipo Grandianda ya ziyarce shi a fadarsa inda ya ce tuni gwamnati ta maido da wasu ‘yan gudun hijira kusan 150,000 gida wadanda suka tsallaka kasashen da ke makwaftaka da Nijeriya sakamakon rikicin.

You may also like