
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Kenya, William Ruto
Gwamnatin Kenya ta fito ta amince kan cewa kasar na fama da ƙarancin kuɗi wanda hakan ya sanya aka samu jinkiri wajen biyan albashin ma’aikatan gwamnati.
Gwamnatin ta ce dole ne ta sanya ta ɗaukan matsaya, tsakanin biyan albashi ko kuma ci gaba da biyan bashin kasashen waje da ake bin ta.
Jami’ai a ma’aikatu da hukumomin gwamnati ne jinkirin biyan albashin ya fi shafa.
Ministan kuɗin ƙasar, Njuguna Ndung’u ya ce gwamnati na fuskantar matsalolin kuɗi saboda ƙarancin haraji da kuma gaza samun bashi.
Tuni ƙungiyoyin ƙwadago biyu na ƙasar suka bayar da sanarwar za su dakatar da ayyukansu saboda matsalar ta jinkirin biyan albashi.
Mataimakin shugaban ƙasar Rigathi Gachagua ya ɗora laifin matsalar ƙarancin kuɗin a kan tsohuwar gwamnatin ƙasar, wadda ya zarga da cin bashi fiye da ƙima da kuma wawushe lalitar ƙasar kafin miƙa mulki a bara.
Sai dai bai bayar da wata hujja ko shaidar da za ta tabbatar da zargin da yake yi ba.
Ƙasar dai na buƙatar kuɗi dalar Amurka miliyan 420 a kowane wata domin biyan albashin ma’aikata.
Yayin da yawan bashin da ake bin ta ya kai kashi 65% na kuɗaɗen shigar ƙasar.